Sanin kowa ne a yankin arewacin NAJERIYA bayan jahar zamfara sai kuma jihar Katsina wajan fama da talauci da kuncin rayuwa da ta'addanci Wanda ke Kara jefa yankin arewacin NAJERIYA cikin kara tabarbarewar rayuwa. Amma duk da wannan yanayi da yankin na arewa yake fama dashi sai muka hango hoto ko video na matar Gwamnan jihar Katsina wato Hajiya Amina Umar Dikko Radda tana cin mutuncin dollars kudi Mai daraja a fadin duniya.
Anya Gwamnonin Arewa ba kune matsalar arewa ba kuwa mutane suna mutuwa saboda rashin abinda zasu ci ko su Sha amma Kuna irin wannan rayuwar KU da iyalanku to Allah ya kwato talaka daga hannun azzaluman shugabanni.